Tsaron Sokoto
Tsaro: Matasa a jihar Sokoto sun sha alwashin kare kansu saboda "sakacin gwamnati"
- By NAGARIFMNEWS --
- Thursday, 04 Sep, 2025

- 175 views
Tsaro: Matasa a jihar Sokoto sun sha alwashin kare kansu saboda "sakacin gwamnati"
Matasa a karkashin kungiyar Shagari Youths a karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto sun yi barazanar daukar matakin kare kansu sakamakon tabarbarewar tsaro a yankin.
Matasan sun kuma zargi gwamnati da sakaci duk da hare-haren âyan bindiga da ake ta fama da su tare da korafe-korafen jamaâa.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin kungiyar ta hannun Bello Bala Shagari, ya bayyana cewa matasan sun yanke wannan shawara ne a wani taro na yanar gizo da suka gudanar ranar Laraba.
Ya ce: âDa dama sun bayyana cewa gwamnati ta gaza wajen cika alhakin kare rayuka da dukiyoyin jamaâa. Saboda haka, kare kai yanzu shi ne kadai zaÉin da ya rage.â
Ya kara da cewa matasan sun yanke shawarar daukar duk wani mataki da ya dace domin kare kansu daga cin zarafi da hare-haren âyan bindiga.
Sai dai Shagari ya bayyana cewa dan majalisar tarayya mai wakiltar Yabo/Shagari, Umar Yusuf-Yabo, ya yi kira da a yi hakuri, a bi doka, tare da samun karin shawarwari.
Duk da ya nuna fahimtar takaicin da matasan ke ciki, ya roki gwamnati da ta hanzarta daukar mataki domin dakile abin da ya ce na iya ârikidewa zuwa barazana mai girma.â
âMatasan sun gaji da jira kuma suna rasa kwarin gwiwa ga hukuma. Tura jamiâan tsaro cikin gaggawa zuwa Shagari zai sake tabbatar da kwarin gwiwar alâumma tare da hana tashin hankali.
âIdan gwamnati za ta amince da tsarin kare kai cikin tsari, matasan Shagari a shirye suke su samu horo yadda ya kamata domin kare kansu da iyalansu a karkashin doka,â in ji sanarwar.
Nagarifmradio




